Pair of Vintage Old School Fru


YAHAYA WEBLEANER IS UNDER WORKING, we are apologise our visitors.

Dan shekaru 3 ya mutu a shadda - Yahaya WEBLEANER

Dan shekaru 3 ya mutu a shadda

Wani yaro dan shekara uku ya rasa ransa
bayan da ya fada cikin masai a kasar Afirka
ta Kudu.
Omari Monono ya mutu ne a wani bandaki
da ke wajen gidansu a lardin Limpopo,
wurin da aka taba samun wani yaro mai
sheharu biyar mai suna Micheal Komape ya
mutu a shadda a shekarar 2014.
"Ina cikin matukar damuwa, ba na iya cin
abinci, ba na iya bacci," a cewar mahaifiyar
marigarin Kwena Monono.
"A kowane lokaci na ga wani abu da yarona
yake so, sai zuciyata ta karaya sai kuma kuka
ya zo mini."
Zaki ya cinye masu farautar karkanda a
Afirka ta Kudu
Thailand : Mai kokarin ceto yaran da
suka makale a kogo ya mutu
An fito da yaron daga cikin shadda a ranar
Laraba ne da misalin karfe hudu agogon
can, sa'o'i biyu bayan bacewar yaron in ji
mahaifiyarsa.
'Yan sanda sun ce innar yaron ta kai
rahoton ne bayan ta neme shi ta rasa.
"Innarsa ta tube shi domin ya shiga ban
daki kamar yadda ta saba sai ta koma cikin
gida domin ta ci gaba da ayyukan gida, daga
bisani sai ta lura yaron bai dawo ba, har
lokaci mai tsawo" in ji wani mai magana da
yawun 'yan sanda, Maphure Manamela.
Masu fafutika sun fara kokarin gannin an
biya iyalan marigayin diyyar Rand miliyan 3
(kimanin dala 221,000).
Wannan al'amarin ya jawo zanga-zanga,
inda mutane ke cewa a rufe shadda domin
kiyaye irin wannan abu daga sake faruwa.
Wannan ba shi ne karon farko da aka samu
faruwar irin wannan al'amari ba, domin a
farkon shekarar nan wata 'yar shekara biyar
ta mutu a shadda a kudancin lardin Cape.

news
Comments:

Post a comment